Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Dakatar Da Aiwatar Da Dokar Harajin Yanar Gizo


Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu
Shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bukaci Babban Bankin Najeriya da ya dakatar da aiwatar da dokar haraji ta yanar gizo da ya dora kan 'yan kasa wacce aka fi sani da cybersecurity levy, sannan ya bayar da umurnin a sake nazarin matakin.

ABUJA, NIGERIA - Sai dai wasu kwararru da masu ruwa da tsaki sun ce a soke tsarin baki daya, kada a sake nazari akai, domin babu wani dalili na dorawa 'yan kasa haraji a halin da ake ciki na matsin rayuwa a kasar.

Kafin Shugaban kasa ya ba da wannan umurni, Majalisar Dokokin kasa ma ta yi zama na musamman akan batun, inda aka samu sabanin ra'ayi a matakan da Majalisar Dattawa da ta Wakilai suka dauka, kan wannan umurni da Babban Bankin Najeriya ya aikawa bankunan kasar.

Babban bankin ya aikawa bankuna cewa su rika karbar kashi 0.5 cikin 100 na kudade a matsayin haraji, domin inganta tsaro ta yanar gizo a kan duk wasu hadahadar na'ura mai aiki da kwakwalwa a kasar.

Majalisar dattawa ta amince da tsarin inda shugaban Kwamitin kula da harkokin tsaro da leken asiri, Sanata Shehu Umar Buba ya ja hankalin ta cewa, harajin tsaro ta intanet din an yi shi ne domin inganta tattalin arzikin kasar, ba don kuntatawa 'yan kasa ba, kuma tana cikin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo wacce aka yi wa gyara a wannan shekara ta 2024.

Saidai, Majalisar Wakilai ta yi watsi da lamarin inda ta ce ba ta amince ba kamar yadda Onarabil Yusuf Shittu Galambi ya shaida w Muryar Amurka cewa tabbas Majalisa ta hana a aiwatar da wannan bukata na babban bankin Najeriya, saboda irin wahalhalu da mutane ke ciki a yanzu.

Galambi ya ce batun sanya haraji a daidai wannan lokaci bai kamata ya taso ba. Galambi ya kalubalanci hujjar da babban bankin ya bayar wai don a tsare wa mutane kudaden su ne daga satar da yan jagaliyar yanar gizo wadanda aka fi sani da yahoo boys su ke yi.

Ya kara da cewa hakkin bankuna ne su kare kudaden jama'a a ko ina cikin duniya ba a Najeriya kadai ba.

Galambi ya ce idan aka yi la'akari da mawuyacin halin tsadar rayuwa da ake ciki, da karin kudin man fetur, da na lantarki da yunwa da talauci da ya yi wa al'umman kasar katutu, bai dace a ce an yi karin haraji ba a wannan lokaci, kuma su a Majalisar Wakilai ba za su lamunta ba

Shi ma Wakilin Kungiyar Transperancy International ta kasa da kasa, Auwal Musa Rafsanjani yayi tsokaci cewa wannan mataki na babban bankin Najeriya ba shi ne zai kare kudaden mutane ba, domin zai sa mutane su daina ajiya a bankuna.

Rafsanjani ya ce dokar kasa ba ta amince a tara Naira triliyan 3 malala gashin tunkiya na kudaden yan kasa kuma a kai su Ofishin Mai ba Shugaban Kasa shawara a harkar tsaro ba, saboda babu abinda ya hada shi da kudaden 'yan Najeriya.

Sai dai shugabar Kungiyar Mata Zalla Hajiya Saratu Sa'a Musawa ta ce tana da shawara ga manyan kasa cewa su hadu daga Kudu da Arewa, Gabas da Yamma su je wurin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu su gaya masa cewa yan kasa fa suna ta mutuwa saboda wahala da yunwa, da cuta da patara, saboda haka ya kawo dauki cikin gaggawa., yan kasa suna cikin wani yanayi. Saratu ta ce ta lura shugaba Tinubu yana jin shawara.

Su ma Kungiyoyin Kwadago ta Najeriya da Cibiyar Bunkasa Kamfanoni Masu zaman kansu NCL sun yi watsi da wannan harajin,tareda lura da hakan zai kara tabarbarewar tattalin arzikin kasar ne.

Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:

Tinubu Ya Dakatar Da Aiwatar Da Dokar Harajin Yanar Gizo.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG