Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Jingine Kudirin Dakatar Da Harajin Tsaron Intanet  


Majalisar wakilan Najeriya (Twitter/ House of Representatives, Nigeria)
Majalisar wakilan Najeriya (Twitter/ House of Representatives, Nigeria)

Majalisar Wakilan Najeriya ta jingine kudirin dake neman dakatar da batun harajin tsaron intanet daya janyo suka da allawadai daga ‘yan Najeriya

Dan Majalisa Manu Soro, daya gabatar da kudirin gaban majalisar a yau Laraba, yace harajin bai zo a lokaci daya dace ba, duba da mawuyacin halin da ‘yan Najeriya ke ciki.

Dan majalisar ya kafa hujja da cewar Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa Akan Harkokin Tsaro mukami ne na siyasa: kuma ba shi da ikon tasrifi da kudaden da aka tara.

Saidai, Kakakin Majalisar, Tajuddeen Abbas, ya bukaci ‘yan majalisar su jingine kudirin domin baiwa shugabanninta damar tattaunawa akan hanyar data fi dacewa a shawo kan lamarin.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Tajudeen Abbas

Batun bijiro ta harajin tsaron intanet din ya gamu da suka da cece-kuce tsakanin ‘yan Najeriya da kungiyoyin fafutukar farar hula.

A cewar sanarwar daya rarrabawa bankunan kasar a ranar 6 ga watan mayun da muke ciki, Babban Bankin Najeriyar ya bayyana cewar harajin zai fara aiki ne nan da makonni 2 masu zuwa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG