Kungiyar Kwadago ta TUC ta yi barazanar kiran gagarumin bore da zai tsaida tattalin arzikin kasar cak, muddin gwamnatin tarayya ta ki janye kudurin ta da ya ja hankalin jama’a, na harajin tsaron kafar sadarwar intanet da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bullo da shi.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Festus Osifo, a ranar Laraba, kungiyar ta yi allawadai da umurnin na babban bankin Najeriyar ga bankuna a fadin kasar su caza kashi 0.5 cikin 100 a matsayin harajin tsaron intanet akan duk wata hada-hadar kudi.
Wannan dai na zuwa ne bayan kakkausar caccakar da takwarata ta NLC tayi akan batun harajin da ta bayyana a matsayin wani karin nauyi a kan yan’ Najeriya.
Batun dai na ta fama da suka tun bayan da CBN din ta ayyana shi, da cewa za a fara cire harajin na tsaron internet din a nan da makonni biyu, tun daga ranar 6 ga watan Mayu.
Kungiyar ta TUC tace, bai yi tsari ba ace a irin wannan lokacin da 'yan Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da aka kakaba musu, sakamakon karyewar darajar naira, tashin gwauron zabbin farashin man fetur da mahaukacin karin kudin lantarki, da dai sauran su, ace kuma za a bijiro da batu irin wannan.
Kungiyar tace ta damu matuka ganin tun da Shugaba Ahmed Bola Tinubu ya zama shugaban kasa, tsare-tsaren gwamnatin shi ba abinda suka kawo wa 'yan Najeriya illa tsanani, masifa da da na sani.
Kungiyar ta kuma zargi Majalisar Dokoki da hada kai da wasu a bangaren zartaswa wajen tatsar talakawan kasa da ya kamata ace suna karewa.
A karshe yace, kungiyar ta bayyana cewa, muradin yan Najeriya a yanzu shine, gaggauta cimma matsaya akan albashi mafi karanci, amma ba wannan mummunan kudurin ba.
Ta kuma bukaci gwamnatin tarayya ta hanzarta umurtar CBN da ya janye umurnin da ya mikawa bankuna da yin fatali da harajin tsaron na internet.
Dandalin Mu Tattauna