Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsarin Harajin Tsaron Intanet Ta CBN Ya Sanya ‘Yan Najeriya Cikin Rudani


Babban Bankin Najeriya CBN
Babban Bankin Najeriya CBN

'Yan Najeriya daga sassan kasar daban-daban ke ta bayyana mabanbantan ra’ayoyinsu da nuna shakku da rashin fahimtar yadda tsarin yake, jim kadan bayan fitowar sanarwar bankin CBN wanda za’a fara aiwatarwa nan da makwanni biyu daga ranar da sakon ya fito.

Kasa da sa’ao’i 24 da babban bankin Najeriya wato CBN ya umurci bankunan kasuwancin kasar da su fara cajin kaso 0.5 cikin 100 na harajin tsaro ta yanar gizo kan hada-hadar kudi, ‘yan Najeriya, musamman masana a fannin kudi da ‘yan kasuwa sun shiga wani irin rudani inda su ke kira ga gwamnati da ta yi musu karin bayani.

Da muka tuntubi shahararren dan kasuwa mai kamfanoni kama daga na gine-gine, samar da kayayyakin abinci ta hanyoyin zamani, Alhaji Jami Abdulsalam ya ce tsarin na CBN zai kara sa wa mutane tsoro har a koma gidan jiya na ajiyar kudadden a gida.

Shi ma babban manajan bankin microfinance na jihar Yobe, Sharrif Muhammad Almuhajir, ya bayyana cewa duk da cewa akwai yiyuwar gwamnati ta dauki wannan sabon mataki ne don kare ‘yan kasa, shi ma bai riga ya fahimci wannan sabon tsarin ba sakamakon a ‘yan watannin baya bankin CBN ya aika wasikar cazar wani haraji na daban.

A wani bangare kuma, masani a fannin mu’amalolin kudi na bangaren addinin Islama wato islamic bankin ya ce idan aka yi la’akari da tsare-tsaren kare asusun kudi a bankuna na kasa da kasa, tsarin na bankin CBN ya saba kuma zai kara jefa al’umma cikin rudani.

Rahotannin dake ta yawo a dandalolin yanar gizo dai sun yi nuni da cewa sabon tsarin na nufin cewa ga masu aika kudadde, za’a rika cajar naira 5 akan dubu 1, naira 50 akan dubu 10, naira 500 akan dubu 100, dubu 5 akan naira miliyan 1, naira dubu 50 a kan miliyan 10 da dai sauransu.

Duk kokarin ji ta bakin bankin CBN a yayin hada wannan rahoton dai ya ci tura bayan tura sakon kar ta kwana amma wasu majiyoyi sun yi nuni da cewa bankin zai wallafa dukkan bayanan da ake bukata ga 'yan Najeriya nan bada jimawa ba shafinsa na yanar gizo.

A saurari cikakken rahoton Halima Abdulrauf:

Tsarin Harajin Tsaron Intanet Ta CBN Ya Sanya ‘Yan Najeriya Cikin Rudani
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG