Cacar baki tsakanin Gwamnatin jihar Bauchi da tsohuwar Majalisar dokokin jihar jihar ya fito fili game da batun bashin kudi Naira miliyan dubu dari hudu wanda Gwamna Muhammad Abdullahi Abubakar ya karbo daga Bankin U .B.A.
A yayin da Gwamnatin jihar Bauchi, ke ikirarin cewa majalisar dokokin jihar Bauchi data shude ita ta amince da a karbo bashin ita kuwa tsohowar majalisar cewa tayi babu wani alaka daya taba hadasu da Gwamnan, hasali ma ta bukaci Gwamnatin data janye wanna furuci kokowa ta garzaya kotu.
Yakubu Ibn Muhammad mai baiwa Gwamna shawara akan alamuran da suka shafi labarai ya ce yana so ya kara maimaitawa cewa kafin a karbo bashin sai da Gwamna ya kama kudirin majalisa ta 7, wace ta gabata wanda kuma wannan kudirin dople sai kakakin majalisa da babban akawun majalisa sun sa hannu tabbas Gwamna ya samu wannan kudirin.
Sai dai kuma a ganawa da manema labarai domin maida martini kakakin kungiyar ‘yan majalisan Abdulmumini Hassan Ningi, ya ce babu wani bukata wanda Gwamnatin M.A Abubakar, ta kawo wace aka amince da ita amma abun takaici sai gashi a cikin jarida kan cewa majalisa ta 7, ce ta tallafa aka karbo bashin to inna tabbatar da cewa babu hannu majalisa domin bamu bada wanna kudiri ba.
Your browser doesn’t support HTML5