Ganawar tsakanin jakadan Amurka da ministan sadarwar Kamaru kuma mai magana da yawun gwamnati suna da mahimmancin gaske.
Jakadan da Ministan sun tattauna ne jiya Alhamis akan matakan da Amurka take dauka domin taimakawa kasar Kamaru wajen yakin da ta keyi da 'yan ta'adan Boko Haram. Ministan yace sojojinsu suna cigaba da yaki a fagen fama kuma suna taka rawar gani saboda akai akai suna samun nasara.
A tattaunawar tasu jakadan Amurka yace wasu kafofin yada labarai na Amurka suna bukatar su ziyarci kasar ta Kamaru saboda su yada labarai musamman akan aikin sojojin dake fagen fama.
Kafofin labaran da jakadan ya keso su kai ziyarar sun hada da New York Times da CBS da CNN.
Tun farko shugaban Amurka ya tura sojoji dari uku zuwa kasar ta Kamaru kuma gwamnatin Amurka na bukatar sanin duk abun dake wakana a kasar dangane da yaki da 'yan Boko Haram.
Ga karin bayani.