Majalisar dattijan Amurka ta kada kuri'ar soke wani kaso mai tsoka na dokar garambawul ga inshoran kiwon lafiya, dokar da ake kallo a zaman ginshiki a nasarorin da shugaba Obama ya samu a cikin gida, da ake kira ACA a takaice, ko da lakabinta na Obamacare.
Haka nan majalisar wacce 'yan Republican suke da rinjaye ta hana kwaskwarimar da 'yan Democrat suka nemi gabatar da zai takaita sayar da makamai, biyo bayan harin da aka kai a jahar California. Haka nan Majalisar ta kada kuri'ar rike kudade da ake baiwa kungiyar da take taimakawa mata su zubda ciki da ake kira Planned Parenthood da turanci.
Amma ba kamar shigen wadannan kudurori da masu yawa da 'yan Republican suka yi a baya ba na neman soke dokar kiwon lafiyar, ko su janye kudaden da za'a aiwatar da shirin, wannan karon babu makawa dokar zata isa tebeurin shugaba Obama, wanda tuni yayi alkawarin zai hau kujerar naki.