Mai martaba sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi ya yi furucin ne yayin da ya karbi kungiyar dake yaki da ayyukan fyade da ta'ammali da miyagun kwayoyi a karkashin shugabancin mai dakin kwamishanan 'yansandan Kano Hajiya Saliha Muhammad Katsina.
A jawabinsa sarkin yace kamata ya yi a hukunta duk wadanda suke da hannu da yin lalata da dalibai maza a dakunan kwanciyarsu a makarantar sakandare ta Hassan Gwarzo. Yace idan ba'a samu kowa ba to ya kamata a hukunta shugabannin makarantar wadanda suke da alhakin kula da lafiyar yaran domin su aka ba amanar daliban. Yace su ba zasu yadda ba sai an hukunta duk wanda yake da hannu a aika-aikar.
Akan batun luadi da aka yi a makarantar sakandare ta Hassan Sani Gwarzo gwamnatin Kano ta kafa kwamitin bincike kuma har yanzu ana jiran sakamakon binciken.
Kwamishanan labaran jihar Kano Malam Muhammad Garba yace har yanzu gwamnati na dakon kwamitin ya mika mata rahoton binciken. Duk lokacin da kwamitin ya gabatar da rahotonsa za'a sanarda al'ummar jihar da ma kasa gaba daya. Kana duk matakan da gwamnati zata dauka za'a bayyanasu fili ba tare da wata rufa rufa ba. Za'a yi hukunci kwakwara kan duk wadanda suke da hannu a lamarin.
Ga karin bayani.