Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara ta Tashi a Kasuwar Sabongarin Kano


Sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi II
Sarkin Kano Muhammad Lamido Sanusi II

Gobarar da ta tashi a kasuwar Sabongarin Kano ta fara ne daga bangaren masu sayar da katako kafin ta bazu ta lakume shaguna hamsin da 'yan kai

Gobarar da ta tashi a yankin 'yan katako na kasuwar Sabongari ta dauki fiye da awa daya wutar na ci.

Inda gobarar ta tashi a daran jiya nan ne kafintoci ke hada hada a kasuwar kuma ta kone kimanin rumfuna hamsin da 'yan kai lamarin da ya haddasa hasarar kaya na miliyoyin nera.

Wani ganao Nuru Haruna ya bayyana abun da ya faru a kasuwar. Yace a daidai wurin da masu sayar da kayan fenti da kayan gida nan abun ya faru. Wutar ta fara ne wajejen karfi bakwai na yamma kuma ta yi ta'adi sosai. Duk kokarin da aka yi a kashe wutar ya cutura.Sai bayan ta yi awa daya da rabi tana ci aka shawo kanta.

Saidai duk da hasarar kaya na miliyoyin nera da aka yi babu wani da ya ji rauni.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:04 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG