Masu bada gudummawa a harkokin tsaro sun soma kira ga gwamnati ta tsananta bincike wajen gano kanana da manyan barayi.
Dr. Muhammad Bello na Jami'ar Tarayya dake Kashere jihar Gombe masani akan lamuran tsaro yana ganin sai an marawa sojoji baya zasu iya cimma nasarar gamawa da 'yan ta'ada nan da zuwa karshen shekarar nan.
Ya nuna damuwa da masu yada labarai ta yanar gizo inda suke karyawa mutane gwuiwa da yakin da sojoji keyi a karkashin Janar Buratai.
Yace yau idan mutum ya je arewa maso gabas ko dan yaro zai fada cewa an samu cigaba a harkokin tsaro saboda shi hafsan hadsoshin kodayaushe yana bakin daga da sojojinsa.
Biyo bayan kama wasu barayin motoci a Abuja shahararren tallafawa 'yansanda wajen kama masu fashi da makami Ali Kwara yace tsoffin barayin kasar sun koma suna gindin 'yan banga ko Fulani. Da zara an yi fada ko da kirista maimakon a zauna a yi sulhu sai su zuga su ce a je a rama. Su ne suke tara Fulani su gaya masu su tara kudi domin a sayo bindigogi. Idan an tara masu nera miliyan goma sai su sayo bindigogin miliyan daya ko biyu sauran kudin kuma su raba tsakaninsu. A kowace jiha suna da gungun manyan barayi da suke aiki dasu suna haddasa rigingimu.
Ali Kwara yace su ne suke koyawa yara su zama 'yan fashi. Wannan lamarin ya bata kasar gaba daya. Bugu da kari lamarin ya kawo hadin kan barayi da masu aika ta'asa. Da an taba daya sai sauran su yi taron dangi su kai ramuwa.
Wannan na faruwa ne daidai lokacin da aka danke wani dan Boko Haram a Zaria sanye da rigunan 'yan agajin kungiyar IZALA. Injiniya Mustapha Siti daraktan 'yan agajin kungiyar yace sun kama wani suka mikashi ga 'yansanda. A wurin 'yansandan ya yi masu bayanin shirin da Boko Haram ta yi na kai hare-hare
Ga karin bayani.