Burtaniya Za Ta Tallafa Wa Yaki Da Boko Haram A Yankin Tafkin Chadi

Burtaniya Za Ta Taimaki Najeriya 2.

Burtaniya ta sha alwashin taimaka wa dakarun kawancen kasashen yankin tafkin Chadi wajen gaggauta kawo karshen mayakan kungiyar Boko Haram da take tafka ayyukan ta’addanci a yankin.

Babban kwamandan rundunar dakarun kawancen kasashen tafkin Chadin, Manjo Janar Ibrahim Manu Yusuf, ya jagoranci manyan jami’an rundunar wurin tattaunawa da jami’an Burtaniya karkashin jagorancin sakataren dake kula da al’amuran siyasa na Burtaniya da suka jibanci yankin tafkin Chadi, Dr. Catherine Probes.

Ganawar ta tabo yanda Burtaniya za ta tallafa wa dakarun kasashen tafkin Chadin a kokarin da kasashen ke yi na kawo karshen kungiyar Boko Haram don samar da kyakkyawar yanayin zaman lafiya da zai samar da ci gaba mai dorewa a wannan yanki.

Burtaniya Za Ta Taimaki Najeriya 3

Wannan ganawar ta kuma bai wa babban kwamandan runduna daman yin Karin bayani dangane da irin gumurzu da suke yi a halin yanzu, nasarori da kuma kalubaloli da suke fuskanta da kuma fannoni da Birtaniya zata iya shigowa dan tallafawa.

Janar Ibrahim Manu Yusuf ya kuma yi wata ganawa ta daban da kwamandan rundunar “Operation Turus” na sojojin Burtaniya, Kanar Nick Abram da kuma kwamadan dakarun Burtaniya da ke tallafa wa kasashen Afrika ta Yamma, Kanar Nick Tom, da nufin fayyace hanyoyin da za su sa hannu don mara wa fafatawa da sojojin tafkin Chadin ke yi a halin yanzu.

Manjo Janar Yakubu Usman, babban hafsan sojin Najeriya mai murabus ya ce inda yakin ya kai, idan aka samu taimakon kayan aiki irin wanda za a iya yaki cikin dare zai taimaka ainun. Haka zalika taimakon kayan yakin zamani za su taimaka sosai.

Burtaniya Za Ta Taimaki Najeriya 1

Wani mai bincike kan sha’anin tsaro a yankin tafkin Chadi da Sahel, Dr. Kabiru Adamu ya bayyana yanda yake kallon wannan ganawa. Ya ce ba kamar irin taimakon da Burtaniya ke yi a baya ba kamar bada horo da kuma kula da dakaru, babban abin da rundunar tafkin Chadin ke bukata shi ne makamai da kuma tattara bayanan sirri.

“Wind Commander” M. I. Salman, masanin tsaro ne wanda kuma ya ce akwai hanyoyi na musamman da yakamata a ce wannan tallafi ya zo. Yana mai cewa a maida hankali a kan batun bayanan sirri, a san inda ‘yan ta’addan suke kana a samu makamai da za a iya mayar musu da martani idan an gano inda suke.

Ga dai rahoton da Hassan Maina Kaina ya aiko mana daga Abuja:

Your browser doesn’t support HTML5

Birtaiya Zata Tallafawa Yaki Da Boko Haram A Yankin Tafkin Chadi

Karin bayani akan: Burtaniya, Boko Haram, Chadi​, Nigeria, da Najeriya.