Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakkabe ‘Yan bindiga Zai Bunkasa Harkar Noma a Najeriya – Manoma


Wasu manoma a gona suka aiki.
Wasu manoma a gona suka aiki.

Manoma a Najeriya sun ce ci gaba da ayyukan kakkabe mahara a yankunan Zamfara da makwabtanta babu kakkautawa za su farfado da harkar noma da ta tagayyara a yankunan.

Kalaman manoman na zuwa ne yayin da dakarun Najeriya ke ikrarin samun nasarori akan ‘yan bindiga da suka addabi wasu dazukan da ke arewa maso yammacin Najeriya musamman a Zamfara da Katsina.

“Saboda haka muna godiya da fatan alheri da su ci gaba da abin da suke yi, kuma wannan da suka yi ya nuna da gaske suke yi. Idan aka dore da yin hakan zuwa wata biyu ko uku nan gaba, alherin da za a samu ba kadan ba ne.” In ji Muhammed Gwazo, wani manomi da ya yi hira da VOA.

Dakarun sama da na kasa na Najeriya sun ce, sun yi nasarar halaka da dama daga cikin masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma sauran dazukan arewacin Najeriya.

Matsalar tsaro a Najeriya ta sa manoma da dama, ba sa iya zuwa gonaki na tsawon lokaci, inda wasu lokuta ma har maharan kan sakawa manoman harajin da za su biya kafin su je gonakinsu.

Hakan kuma ya kassara samar da amfanin gona a sassan Najeriya musamman a arewaci wanda ya dogara da harkokin noma

“Mu shwarar da muke bayar wa ita ce, gwamnatin ta nuna da gaske take yi, don a dawo da noma, wallahi idan babu noman nan kasar nan za ta shiga wani yanayi.” Gwazo ya kara da cewa.

Faruku Ahmed Gusau, manomi a Gasau, ya yi kira ga manoma da su yi shirin komawa bakin aiki lura da yadda ake samun nasara akan maharani da ke satar manoma don neman kudin fansa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG