Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana

Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya jaddada muhimmanci aiwatar da taron ƙolin ƙasashen yankin tekun Guinea wato "Gulf of Guinea Commission" mai fafutukar kare yankin daga ayyukan masu fashin teku.

KUMASI, GHANA - Abin da shugaba Buhari ya ce zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da inganta tsaron yankin. Buhari na jawabin ne yayin wani taron kolin ƙasashen yankin tekun Guinea da aka gudanar an Accra babban birnin kasar Ghana ajiya Talata.

Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana

Shugaban ya kara da cewa ''tilas ne a garemu da mu ƙarfafa tarukan ƙungiyar ƙasashen yankin tekun Guinea da na shugabannin ƙasashen yankin domin samun damar tattauna matsalolinmu tare da lalubo hanyoyin magance su, domin samar da zaman lafiya, da tsaro da kuma ci gaban ƙasashen yankin tekun Guinea'', in ji shi.

Shugaban ya tabbatarwa mambobin kungiyar kasashen cewa tarayyar Najeriya ta cimma nasarori da dama wajen yaƙar ayyukan masu fashin teku a yankin tekun Guinea, tare da bukatar da ƙasashen ƙungiyar da su samar da dokoki da za su haramta fashin teku, kamar yadda Najeriya ta yi.

Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana

Tsohon babban jami'i a dakarun soja na kasar Ghana kuma mai sharhi kan harkar diflomasiyya da kuma tsaro Umar Sanda Ahmad ya bayyana cewa wannan shawara da shugaba Muhammadu Buhari ya bayar ko shakka babu shine mafi a'ala.

"Hadin guiwa tsakanin kasashen da ke yankin tekun Guinea kamar yadda shugaba Buhari ya bukaci zai yi taimako sosai kuma ya rage matsalolin da kasashen ke fama da su domin idan jirgin ruwa ya taso daga Najeriya zuwa Ghana idan aka tare shi ba Najeriya ka dai zatayi asara ba harda Ghana, adon haka idan ba a tashi da sauri an magance matsalan fashin teku ba zai maida kasashen baya"

Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana

Shi kuwa shugaban Ghana Nana mai masaukin baki kana wanda ya jagoranci taron ya bukaci da mambobin kasashen da suyi kokarin bada nasu gudunmuwa wajen tabbatar da shawo kan matsalan ‘yan fashin teku, abin da ya ce shine hanya daya tilo da zai taimaka wajen karfafa tsaro da ci gaban kasashen.

Taron kolin kasashen yankin tekun Guinea da ake gudanarwa ya fuskanci koma baya tun lokacin da cutar COVID-19 ta zamo annoba.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

Buhari Ya Halarci Taron Kolin Kasashen Yankin Tekun Guinea A Ghana.mp3