Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

 Kasashen Afirka Rainon Faransa Sun Yi Taro Kan Batun Gindaya Ka'ida A Yanar Sadarwa

 Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo
Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo

Shugabannin hukumomin sadarwar kasashen Afirka rainon Faransa, mambobin kungiyar REFRAM, sun gudanar da taro a Nijar don tattaunawa kan batun samar da dokoki na bai daya na amfani da yanar sadarwa.

NIAMEY, NIGER - Duk da ci gaban da yanar sadarwa ta zo da shi, inda kusan kowane fanni ya ta'allaka kan intanet, bayanai daga sassan duniya na nuna yadda wannan sabuwar fasahar sadarwa ke haifar da rudani, musamman a kasashe masu tasowa, sakamakon yadda wasu ke amfani da yanar sadarwar ta hanyoyin da ba su dace ba don cimma munanan manufofi.

Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo
Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo

Taron, wanda a wani bangare ke zama na kara wa juna sani a tsakanin shugabanin hukumomi sadarwar kasashe rainon Faransa da kwararru akan sha’anin doka, ya gano cewa rashin dokoki ne babban dalilin da ke bai wa wasu damar cin karensu ba babbaka a irin wadannan kafafe, saboda haka ya zama dole a gaggauta daukar matakan saka tsari.

Rashin kayan aikin wata matsala ce ta daban da ke tauye ayyukan hukumomin sadarwa a kasashe masu tasowa kamar yadda shugaban hukumar sadarwar kasar Cameroun CNC Joseph Chebonkeng Kalabubse ya shaida mana.

Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo
Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo

Ya ce rashin na’urorin zamani ita ce matsala ta farko da ke yi mana shinge wajen dakile miyagun abubuwan da ake yadawa a kafafen yanar sadarwa sannan kamfanonin intanet ‘yan kasuwa suna da buri da dama, bukatarsu ta farko su sami kudi amma ba sa binciken abubuwan da ake yadawa.

Ya ce, mu hukumomin sa ido, mu ne ke da damuwa akan abin. Abu ne da ya mamaye mu domin a lokacin da aka kafa dokokin farko ba a yi tsammanin al’amura za su yi tsanani kamar yadda ake gani a yau ba hatta kasashen da suka ci gaba suna fama da wannan matsala sakamakon yadda ci gaban kimiyya ke ruruwa tamkar wutar daji.

Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo
Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo

An gudanar da wannan taro a wani lokacin da hukumar sadarwar Conseil Superieur de la Communication ta Nijar ta aike wa gwamnatin kasar kudirin doka domin gabatar da shi wa majalisar dokoki wace ke da alhakin kaddamar da shi a matsayin dokar saka tsari a kafafen da ke da alaka da yanar sadarwa.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

 Kasashen Afirka Renon Faransa Sun Gudanar Da Taron Neman Hanyoyin Tsari A Yanar Gizo.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG