Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Na Tattauna Yadda Ake Samun Karuwar Tashe-tashen Hankula A Afirka


Yan Sandan Kasar Senegal
Yan Sandan Kasar Senegal

Kwararru kan harkokin tsaro na gudanar da taro cikin wannan mako a kasar Senegal, domin tattaunawa kan yaki da ta'addanci da ke kara ta'azzara a nahiyar Afirka, musamman a yankin Sahel, inda hare-haren ta’addanci ke karuwa.

A cikin shekaru goma da suka gabata, an zuba dimbin albarkatun da suka hada da sojoji da makudan kudade a yakin da ake yi da tashe-tashen hankula a Afirka.

An gudanar da tarurruka masu yawa, tare da atisayen horarwa don tattauna musabbabi da mafita. Matsalar ba kawai ta ci gaba ba amma ta yi muni.

Kashe-kashen da ake dangantawa da ‘yan ta’adda masu ikirarin jihahi a Nahiyar, ya kai kusan kashi 50 cikin 100 a cikin shekarar da ta gabata, zuwa sama da mutane 19,000, yawancinsu a yankin yammacin Sahel, a cewar Cibiyar Nazarin Dabarun Afirka.

Har ila yau tashin hankalin ya kara fadada zuwa wasu yankuna, kamar kasashen yammacin Afirka da yankin tafkin Chadi.

Giovanie Biha shi ne shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka da yankin Sahel.

Ya ce, "Ba wani sirri ba ne cewa yanayin tsaro a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka na ci gaba da tabarbarewa." "Kungiyoyin ta'addanci na ci gaba da amfani da kalubale iri-iri da ke fuskantar yankin, musamman raunin muhalli, siyasa da zamantakewa da rashin daidaito."

A cikin shekarar 2015, Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar da wani shirin rigakafin ta'addanci don dakile tashe-tashen hankula. Taron na wannan makon zai yi nazari ne kan wannan shiri da kuma tantance yadda kowane yanki da kasashe za su fi aiwatar da dabarunsu.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka da Sahel, da Sashen Harkokin Waje na Tarayyar Switzerland da Cibiyar Nazari kan Tsaro ta Senegal ne suka shirya taron.

Albert Kan-Dapaah shi ne ministan tsaron kasa a Ghana. Ya ce ita ce kasa daya tilo da ke gabar tekun Afirka ta Yamma, da ba ta samu labarin hare-haren masu tsattsauran ra'ayi ba.

Ko da yake Kan-Dapaah ya yarda cewa ba zai iya tabbatar da dalilin da ya sa Ghana ta yi nasarar gujewa tashin hankali ba, ya ce kasar ta aiwatar da tsarin kasa bisa shirin Majalisar Dinkin Duniya bayan an sake shi.

Wakiliyar Muryar Amurka a kasar Senegal, Annika Hammerschlag, ta hada wannan rahotan.

XS
SM
MD
LG