Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Amurka Ya Bude Taron Koli Na Dimokaradiya Karo Na Biyu


Babban Taron Koli Na Domokaradiya Da Shugaba Joe Biden Ya Bude a Karo Na Biyu
Babban Taron Koli Na Domokaradiya Da Shugaba Joe Biden Ya Bude a Karo Na Biyu

Shugaba Joe Biden ya bude taron koli na Dimokuradiyya karo na biyu a jiya Laraba, inda ya yi alkawarin cewa Amurka za ta kashe dala miliyan $690M a shekara mai zuwa domin bunkasa shirye-shiryen dimokradiyya a fadin duniya.

Biden ya ce “Muna kyautata halin da ake ciki a nan. Kamar yadda muka saba fada, muna kan wani matsayi a tarihi a nan, lokacin da shawarar da muke yanke a yau za ta shafi yanayin duniyarmu na gomman shekaru mazu zuwa na tabbata.”

Fadar White House ta lura cewa Amurka musamman tana son sanya “fasaha ta yi fa'ida ga dimokaradaiyya, ba ta yi illa ga dimokoradiyya ba.”

"Muna daidaita halin da ake ciki a yanzu. Kamar yadda muka saba fada, muna kan wani matsayi a tarihi a yanzu, shawarar da muka yanke a yau za ta shafi yanayin duniyarmu na shekaru masu zuwa na tabbata," a cewar Biden.

Wasikar ta ce "Tsarin fasaha irin naku sun zama fagen daga, kuma kasashen waje masu adawa da juna suna amfani da su wajen yada labaran karya wadanda suka saba wa rahotanni daga kafafen yada labarai na gaskiya," in ji wasikar.

"Ana amfani da tallace-tallacen da aka biya kudade da kuma labaran da na’urori ke kirkira a kan dandamalin Meta, ciki har da Facebook, na yin kira ga tarzoma a zamantakewa, kawo tashin hankali a tituna da kuma lalata gwamnatoci."

Kimanin shugabannin kasashen duniya 120 ne ke halartar babban taron kolin, yunkurin Biden na karfafa matsayin dimokaradiyya ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatoci masu cin gashin kansu suka cimma manufofinsu, kamar mamayewar watanni 13 da Rasha ta yi wa Ukraine, da China yunkurin China na hada kai da Moscow.

Gabanin gajerun jawabai daga shugabannin kasa da ke bayyana tsarin dimokuradiyya a kasashensu, Biden da shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol, sun fada a cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa cewa, "Karfafa gaskiya, gudanar da mulkin da ya samo asali daga amincewar wadanda ake mulka muhimmin muhimmin lokaci ne na zamaninmu."

Fadar White House ta ce sabon tallafin da Amurka za ta bayar, bisa amincewar majalisar dokoki, zai mayar da hankali ne kan shirye-shiryen da ke tallafawa kafafen yada labarai masu zaman kansu, da yaki da cin hanci da rashawa, da karfafa 'yancin dan Adam, da ci gaban fasahar da za ta inganta dimokaradiya, da kuma goyon bayan gudanar da zabe cikin 'yanci da adalci.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG