A cikin kwanakin dai an samu irin wadannan hare-haren na sari ka noke a yankin Gombi da Hon, lamarin da ya jawo asarar rayuka dayawa, baya ga gidajen da maharan Boko Haram din ke Konawa. Sai dai kuma a wannan karon maharan sun gamu ne da dakarun soja dake Gombi, wanda yake haryanzu ba’a bayyana adadin mutanen da wannan lamari ya shafa ba, kama daga bangaren soja, Boko Haram, da kuma farar hula.
Dayawa mutanen garin sunyi gudun hijira zuwa cikin daji don gudun abinda ka iya faruwa. Wasu daga cikin masu gudun hijarar sun shaidawa wakilin Ibrahim Abdul’Aziz, cewa garin Gombi babu dadi kuma a yanzu haka suna bayan gari, domin maharan sun shigo cikin garin suna harbe harbe, amma sojoji na kokarin bugawa dasu babu ja da baya.
Hukumomi a jihar dai sun tabbatar da wannan hari da aka kai, inda ma suka bukaci jama’a musammam ma wadanda ke kan iyakar kasar Kamaru da kuma jihar Borno, da ayi taka tsan tsan ganin cewa yanzu maharani na fitowa ne daga yankin Sambisa, sakamakon barin wutar da akeyi musu.
Kakakin gwamnan jihar Adamawa, ya bukaci jama’a da runka bada hadin kai, ya kuma yi gargadi ga jama’a bisa ga abinda ke faruwa a dajin Sambisa, da a rika lura duk wanda ba’a yarda da shi ba to a shaidawa jami’an tsaro, domin kuwa duk wadanda aka koro daga wannan dajin to zasu shigo garine dauke da makamai a jikinsu, don haka mutane su guji yawace yawace.
Wannan na zuwa ne yayinda dakarun soja ke samun nasara akan mayakan Boko Haram, inda har suka kwato yawancin manyan garuruwan dake hannun ‘yan bindigar dake arewacin jihar Adamawa, yayin da a bangare guda kuma kungiyar Boko Haram ke mika mubayarsu ga shugaban kungiyar ISIL dake fafutukar tabbatar da daular islama a kasashen Siriya da Iraki.
Your browser doesn’t support HTML5