Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Chadi Da Nijar Sun Kwato Garin Damasak


Wasu sojojin kasar Chadi a wani gari da ke kan iyaka da Najeriya
Wasu sojojin kasar Chadi a wani gari da ke kan iyaka da Najeriya

Bayan kaddamar da wani hari da su ka yi a ranar Lahadin da ta gabata, dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Nijar sun yi nasarar kwato garin Damasak da ke Najeriya.

Dakarun hadin gwiwa daga kasashen Chadi da Nijar sun kwato garin Damasak da ke hanun kungiyar Boko Haram a jahar Borno ta arewa maso gabashin Najeriya.

A karshen makon da ya gabata kungiyar ta Boko Haram ta ce ta yi mubaya’a da kungiyar ISIS mai ta da kayar baya a Iraqi da wasu yankunan Syria.

Rahotannin sun cewa masu magana da yawun sojojin kasar Chadi sun tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya yi sanadiyar mutuwar ‘yan kungiyar su 200.

Akalla sojojin Chadi 10 aka kashe yayin da 20 su ka samu raunuka, ko da ya ke ana samun bayanai masu karo da juna, inda hukumomin Diffa da ke kusa da garin su ka ce sojojin Chadi 33 a ka raunata.

Sai dai hukumomin Diffa sun tabbatar da cewa an karbi garin daga hanun ‘yan kungiyar a samamen da dakarun hadin gwiwar su kaddamar a ranar Lahadin da ta gabata.

Wannan ba shi ne karon farko da dakarun su ka kwato gari daga hanun 'yan kungiyar ba, ko a makwannin da su ka gabata ma sun kwato garin Dikwa daga hanun masu ta da kayar bayan.

XS
SM
MD
LG