Gwamna Ibrahim Kashim Shettima ya ce gwamantin Jihar za ta taimakawa dukkanin wadanda hare-haren da aka kai a karshe mako ya rutsa da su.
Shettima ya ya bayyana hakan ne a yayin da ya kai ziyara a asibitocin da aka kwantar da mutanen.
A 'yan kwanakin nan ma gwamnan ya bayyana shirin gwamantin sa na gyara gidajen da aka kona da gina rijiyoyin burtsatsai da tone nakiyoyin da 'yan ta'ada ke binnewa.
Game da garin Baga gwamnan ya ce an kona rabin garin kana kuma tsakanin garin da wani dan kauye sojoji sun ka cire naiyoyi 150.
Dangane da alkawarin da gwamnan ya yi can baya cewa zai kwaso duk 'yan jiharsa daga inda su ke gudun hijira, ya ce idan ya gama da kwasar wadanda su ke kudancin jihar zai karkata zuwa Jamhuriyar Nijar.
Akwai mutanen kananan hukumomi biyu da ke zaune a kasar. Ya ce za su je su yi wa gwamnatin Nijar godiya saboda taimakon da suka yi.
Dangane da yunkurin da sojoji ke yi yanzu gwamnan ya ce babu laifi suna iyakar kokarinsu.