Duk da cewa a wasu sassan hukumar zabe ta INEC ta yi ikirarin raba katunan zaben kusan kashi casa'in cikin dari, ta sake kara wa'adin raba katunan har zuwa ranar 22 na wannan watan, wato kwana shida ke nan kafin yin zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.
Jami'in hukumar ta INEC, Kayode Idowu, ya nuna nasarar yin aMfani da na'urar tantance masu kada kuri'u.
Haka kuma wasu 'Yan jam'iyyu sun nuna goyon bayansu da kara wa'adin raba katunan da cewa za su samu nasara a zabukan.
Alhaji Sani Haliru Maiwa, na jam'iyyar APC, ya ce nuna muhimmancin yin zaben ba tare da yin magudi ba.
Ya ce su suna tare da jama'a kuma ba za su taba yadda sojoji su zo su nuna musu bindiga domin su ji tsoro ba.
Hauwa Muhammad, shugabar mata matasa ta APC, ta ce ran da aka ce Janar Buhari ya ci zabe wahalolin jama'a za su kare saboda shi Buhari mutum ne mai kishin kasarsa da talaka.
Shi ma mataimakin daraktan kemfen din PDP, Yariman Muri Isa Tafida Mafinda, ya ce PDP ba ta yiwa INEC katsalandan ba.
Dangane da zargin cewa PDP ta na daukan wasu matakan hana zabe, Mafindi ya ce su ba su taba daukar wata matakala ta hana zabe ba.
Ya kuma kara da cewa shi bai yi tsammanin kafofin labaru irin su Muryar Amurka za su dauka ba domin a ganin sa ba magana ce da masu hankali za su yi amfani da ita ba.