Sojojin Nijar da Chadi sun kaddamar da hare-hare na hadin gwiwa kan kungiyar Boko Haram wacce ta ke da cibiya a Najeriya.
Majiyoyi na soja sun ce a safiyar jiya Lahadi ne sojojin Najeriya da na Chadi su ka fara kai farmakin a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Kasashen biyu sun hada karfi da Najeriya da Kamaru na kai farmaki kan kungiyar wacce ta yi mubaya'a ga kunigyar ISIS.
A ranar Asabar wani dandalin masu ikirarin su ma'abota jihadi ne ya ambaci kungiyar Boko ta na cewa "muna mu'baya'a ga khalifa' a cikin wani fefen bidiyo da a ke ikirari na kungiyar 'yan tawayen Najeriya ne."
Muryar da a ka ji, wacce ta ke ikirarin muryar shugaban kungiyar Boko Haram ce Abubakar Shekau, ta ci gaba da cewa "Za mu ji kuma mu amince ko mutunta shugaban kungiyar ISIS Abu Bakr al-Baghdadi, a na cikin jin dadi da annashuwa ko anan cikin mawuyacin hali da wahala.....".
Sanarwar da Boko Haram ta bayar ranar Asabar, an ba da ita ne sa'o'i bayan fashe-fashe sun rufe Maiduguri babban birnin jihar Borno, har mutane 55 su ka halaka, wasu 140 kuma su ka jikkata.