Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS: Abin da Ya Sa Boko Haram Ta Yi Mubaya’a


Wani wuri da kungiyar Boko Haram ta kai hari a arewa maso gabashin Najeriya
Wani wuri da kungiyar Boko Haram ta kai hari a arewa maso gabashin Najeriya

A karshen makon da ya gabata ne Kungiyar Boko Haram da ke ta da kayar baya a Najeriya ta yi mubayi'a ga kungiyar ISIS mai da'awar kafa daula musulunci. Ko ya ya masana su ke kallon wannan mataki da kungiyar ta dauka?

Masana da masu shaRhi da dama a sassa daban daban na duniya na ci gaba da yin tsokacin kan mubayi’ar da kungiyar Boko Haram ta yi ga kungiyar ISIS.

Kungiyar Boko Haram ta jima na ta da kayar baya a arewacin Najeriya yayin da ayyukan kungiyar ISIS ita ma ta yi kaurin suna wajen kai hare-hare a kasashen nSyria da arewacin Iraqi.

Mubayi’ar da Boko Haram ta yi na zuwa ta zo ne a karshen makon da ya gabata a lokutan da a ka zargi kungiyar da kai wasu munanan hare-hare a jahar Borno.

Boube Na Maiwa, mai sharhi ne akan abubuwan da su shafi siyasa, ya kuma ce taran dangin da kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru su ka yi musu, shi ya sa ita ma kungiyar ta Boko Haram ta waiwayi takwararta ta ISIS.

“Dabara ce su ka sauya, wato su ma su je ‘yan uwans da ke da ra’ayi irin na su su nemi taimako.” In ji Boube.

A cewar Boube, taimako su ke nema domin su fita daga kangin da su ka shiga a ‘yan kwanakin nan.

Garuruwa da dama dai su kubucewa kungiyar ta Boko Haram wadanda da su ke iko da su bayan da dakarun kasashen hadin gwiwa su ka kai musu hare-hare.

Sai dai mai fashin bakin ya ya yi gargadin cewa akwai bukatar kasashen da ke yakar kungiyar ta Boko Haram su zauna cikin shiri domin “za a shiga wani irin hali na dabam wanda za a dinga aiko ‘yan daidaikun mutane” sun a saka bam.

ISIS: Abin Da Ya Sa Boko Haram Ta Yi Mubaya'a - 7'15"
please wait

No media source currently available

0:00 0:07:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG