Akalla mutane 11 ne suka rasa rayukansu bayan wani hari da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Gamboru da ke jihar Borno.
Wannan harin ya biyo bayan kwato garin da dakarun kasar Kamaru suka yi ne makwanni kadan da suka gabata.
Wadanda suka shaida harin da ya faru a ranar Larabar da ta gabata, sun ce, bayan da dakarun Kamaru suka janye daga garin ne aka kai harin saboda garin ya kasance babu tsaro.
Wannan hari wanda ya auku a kusa da kan iyakokin Najeriya da Kamaru, na kara nuna yadda matsalar tsaro ke kara yin katutu a arewa maso gabashin Najeryar, yayin da kasar ke tunkarar manyan zabuka a ranar 28 ga wannan wata na Maris.
Garin ya kasance a hanun ‘yan kungiyar tun a karshen shekarar da ta gabata, kuma har sai a karshen watan da ya gabata ne dakarun na Kamaru suka samu damar kwato shi garin.
Kamaru na daya daga cikin kasashe uku da ke makwabtaka da Najeriya, wadanda suka aike da sojojinsu domin yaki da kungiyar ta Boko Haram.
Najeriya da Chadi da Kamaru da Nijar sun kaddamar da hare-haren hadin gwiwa akan ‘yan kungiyar a watan Janairun da ya gabata bayan da mayakan suka karbe ikon wani sansanin dakarun hadin gwiwa a kusa da Tafkin Chadi.
A makon da ya gabata Sojojin Najeriya sun gayawa Muryar Amurka cewa akwai dakaru daga kasashen Afrika ta Kudu da Burtaniya da kuma Ukraine suna marawa dakarun kasar baya.
Sai dai hukumomin kasar sun ce sojojin suna horar da na Najeriya ne kan yadda za su yi amfani da sabbin makaman da aka saya musu.