Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Borno a Jihar Difa Kasar Nijar


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

Gwamnan jihar Borno ya kai ziyarar gani da ido jihar Difa cikin kasar Nijar inda 'yan gudun hijira daga Najeriya suka yi katutu

Yawancin 'yan gudun hijiran dake kasar Nijar musamman wadanda suke Difa 'yan asalin jihar Borno ne.

Gwamnan Bornon ya zanta da Muryar Amurka akan wannan ziyara ta musamman.

Gwamnan yayi farin ciki da yadda gwamnatin Nijar ta karbi 'yan gudun hijiran tana kuma kulawa dasu. Ya godewa gwamnatin kasar da ta jiha. Ya yiwa kungiyoyi dake zaman kansu da su ma suka taka rawar gani wurin kulawa da bayin Allah da suka tagayyara sabili da rikicin da Boko Haram ta haddasa masu.

Gwamnan yace duk wani taimako da suka kai sun mikawa gwamnatin jihar ne ganin yadda suka yi watanni fiye da biyar suna kulawa da 'yan gudun hijran. Duk wani dawainiya nasu gwamnatin kasar ta keyi.

Akan dalilin da ya sa sai yanzu ya ziyarci 'yan gudun hijiran, gwamna Shettima yace akwai wani lokaci da zuwa kasar Nijar yayi wuyi. Abu na biyu sun sha fama da matsaloli a jihar Borno. Sabili da wadannan dalilan ya sa bai iya ziyartarsu ba amma ba wai ya manta dasu ba ne. Yace duk da rashin zuwansa ya turo tawagar gwamnati ba sau daya ba da kayan agaji kafin shi kansa ya je ya yiwa gwamnatin kasar godiya tare da ganin irin halin da mutanensa ke ciki.

Bayan wannan ziyarar gwamnan yana shirin zuwa kasar Kamaru inda nan ma akwai 'yan gudun hijira da dama kodayake ya tura jami'an gwamnati sau biyu. Yace zai je ya gansu ya kuma basu hakuri.

Ga rahoton Haruna Dauda Biu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG