Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kwato Bama


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Rundunar sojojin Najeriya tayi ikirarin kwato garin Bama, gari na biyu mafi girma a jihar Borno.

Rundunar sojan Najeriya tace ta kwace garin Bama daga hannun mayakan sakai masu ikirarin Islama wadanda suka kama kuma suka ci gaba da rike garin tun a watan Satumban bara.

Rundunar a shafinta na Twitter ta fada jiya Litinin cewa "sojojin Najeriya Litinin din nan sun kori 'yan ta'dda daga garin Bama a jihar Barno. Ana ci gaba da ayyukan kakkabe garin". Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta gaskanta wannan ikirari.

Bama ne birni na biyu a girma a jihar Barno mai tazarar kilomita 65 daga fadar jihar Maiduguri.

Haka nan a jiyan, sojojin kasar sun ce sun gama da 'yan Boko Haram jihar Yobe, makwabciyar jihar ta Barno, bayan da suka kwato garin Goniri.

A ranar Jumma'a, rundunar mayakan kasar ta bada labarin cewa dakarunta sun kawace gari na karshe dake hannun Boko Haram a jihar a arewa maso gabashin jihar Adamawa.

Wadannan jhohi uku sune suka fuskanci galibin tarzomar da 'yan binidgar suke haddasawa cikin shekaru shida na tada kayar baya da suke yi.

A baya bayan nan 'yan binidgar sun fadada hare harensu zuwa kasashe makwabta da suka hada da Nijar, da Cadi da kamaru. Lamari da ya janyo hadin guiwa tsakanin dakarun kasashen hudu wajen yakar Boko Haram.

XS
SM
MD
LG