Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kwato Garin Madagali


Sojojin Najeriya akan wata motar yaki a lokacin da suke zagaye a wata karamar kasuwa a birnin Maiduguri.
Sojojin Najeriya akan wata motar yaki a lokacin da suke zagaye a wata karamar kasuwa a birnin Maiduguri.

A ciga da samun nasara da su ke yi, dakarun Najeriya sun ce sun yi galabar kwato garin Madagali da ke Jahar Adamawa daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta ce ta kwato garin Madagali da ke Jahar Adamawa, wanda shi ne gari na karshe da ke hannun ‘yan kungiyar Boko Haram.

Rundunar ta bayyana hakan ne a shafin sadarwanta na Twitter, inda ta bayyana cewa ta fattaki ‘ya’yan kungiyar daga garin.

A wata hira da ya yi da VOA a farkon makon nan, shugaba Najeriya Goodluck Jonathan, ya yi hasashen cewa dakarun kasar za su kwato ragowar yankunan da ke hanun ‘yan kungiyar a Jihohin Adamawa da Yobe a tsakiyar mako mai zuwa.

Samamen da dakarun hadin gwiwa su ka kai, ya taimaka wajen korar ‘yan kungiyar daga yankunan da suka kwace a arewa maso gabashin Najeriyar, inda rahotanni ke nuna cewa dakarun Chadi da Nijar da na Kamaru sun taka muhimmiyar rawa wajen karbe ikon garuruwan.

Har ila yau shugaba Jonathan ya tabbatar da cewa akwai wasu dakaru da ba na yankin Afrika ba, wadanda ke taimakawa a wajen kai wadannan samame.

XS
SM
MD
LG