Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Yan Gudun Hijira a Jihar Adamawa Sun Koma Garuruwan su


Yan gudun hijira na komawa garuruwan su
Yan gudun hijira na komawa garuruwan su

Wasu Yan Gudun Hijira Sun Fara Komawa Garuruwan su a Jihar Adamawa

Anga yan gudun hijira na jihar Adamawa na komawa garuruwan su bayan da rundunar sojan Najeriya tayi nasarar kwato garuruwan nasu daga hannun yan boko haram

Wakilin sashen Hausa Sanusi Adamu ya bayyana cewa yaga yan gudun hijirar a hayin gada tare da yan yiwa kasa hidima cikin motocin safa-safa, mafi yawan su tsofaffi, gwauraye da kuma marayu, kan hanyar su ta komawa kananan hukumomin madagali, mincika mubi, da dai sauran garuruwa da sojojin hadin gwiwa na kasa da kasa da yan kato da gora suka anso hannun yan boko haram.

Wannan baiwar ALLAH da bata so a ambaci sunan ta ba tace an kashe mijin ta da maghaifin ta kuma an sace mata daya daga cikin yayan ta 5,

“Cikin yara biyar daya shekarun sa 11, daya kua shekarun sa 7, daya shekara 5 wannan shekara 2, duk ba abinda na fita dashi an kone dukiyar mu, sun wuce da shanu biyu da mashin da dukiyar da ya ajiye, ko zani daya ban fiya dashi ba’’

Wakilin sashen Hausa yace wasu daga ciki wadanda yaso yayi hira dasu idanun su cike da hawaye, ga dai Salihu da Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG