Bayern Munich Ta Kammala Sayen Sadio Mane

Dan wasan Liverpool Sadio Mane

“Ina mai matukar farin cikin kasancewa tare da FC Bayern a birnin Munich,” Mane, wanda dan asalin Senegal ne ya fadawa shafin labarai na yanar gizon fcbayern.com.

Dan wasan Liverpool Sadio Mane, ya kammala sanya hannu a kwantiraginsa a Bayern Munich akan fam miliyan 35.1

Dan shekara 30, Mane wanda ya rage masa wata 12 a kwantiraginsa da Liverpool, ya sanya hannu ne akan kwantiragin shekara uku a gasar ta Bundesliga kamar yadda AP ya ruwaito.

“Ina mai matukar farin cikin kasancewa tare da FC Bayern a birnin Munich,” Mane, wanda dan asalin Senegal ne ya fadawa shafin labarai na yanar gizon fcbayern.com.

“Mun yi doguwar tattaunawa, kuma na ga shaukin da wannan kungiya ta nuna a kaina tun daga farko, kuma ni ban taba shakku kan wannan zabi da na yi ba.

“Wannan shi ne lokaci da ya dace na fuskanci wannan kalubale. Ina so na cin ma abubuwa da dama a wannan kungiya da kuma matakin kasa da kasa.” In ji Mane.