Ana ta samun rahotanni da ke nuni da cewa mai yiwuwa, wasan karshe na gasar zakarun turai da za a buga ranar Asabar a Paris tsakanin Real Madrid da Liverpool, shi ne zai zama wasa na karshe da Sadio Mane zai bugawa Liverpool.
Batun makomar dan wasan, wanda dan asalin kasar Senegal ne, ya zamanto babban al’amari a ranar Juma’ar nan yayin da manajan Liverpool Jurgen Klopp yake taron manema labarai a filin wasa na Stade de France a Paris.
Ko da yake, Klopp, ya gujewa saurin zartar da hukuncin cewa Mane zai ci gaba da zama a kungiyar ta Liverpool, yayin da rahotanni ke nuni da cewa zakarun Jamus, Bayern Munich na zawarcinsa.
“Yanzu ba lokaci ba ne da ya dace a yi magana kan wannan batu, duk kungiyar da Sadio zai bugawa a kaka mai zuwa, ba shakka, zai zamanto babban dan wasa.” In ji Klopp kamar yadda AP ya ruwaito.
Mane, wanda ya koma Liverpool a shekarar 2016, na da shekara daya kafin kwantiraginsa ya kare, kuma cikin ba’a ya ce sai an kammala wasan karshe na UEFA, zai ba da amsar ko zai zauna a Liverpool, ko zai kara gaba.
“Ku dawo ranar Asabar, zan ba ku amsar da kuke so ku ji.” Mane ya ce cikin raha.