Wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a nahiyar Afirka guda biyar za su tattaro gaggan kasashen nahiyar a ranar Juma’ar nan.
Daya daga cikin wasannin da suka fi jan hankali shi ne sake haduwa da zaratan ‘yan wasan Liverpool Mohamed Salah da Sadio Mane za su sake yi.
Wasan farko za a buga shi ne a binrin Alqahira na kasar Masar.
A watan Fabrairu ‘yan wasan suka hadu a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika da Kamaru ta karbi bakunci inda Senegal ta doke Egypt.
Senegal ta lashe kofin bayan doke Egypt da ci 4-2 a bugun fenariti.
Ko da yake, ba wasan na Egypt da Senegal ne kadai zai fi daukan hankali ba, akwai sauran manyan wasannin guda hudu da su ma za a fafata.
Najeriya za ta kara da makwabciyarta Ghana, Kamaru za ta hadu da Algeria.
Kazalika Congo za ta hadu da Morocco, sai kuma Mali ta hadu da Tunisia.
Daga cikin wadannan wasanni, kasashe biyar kadai za su wakilci Afirka a gasar ta cin kofin duniya wacce za a yi a Qatar a wannan shekarar.