Shugaban ya ‘kara da cewa gwamnatin Najeriya ta yi nasarar karya lagon su, tare da hana su mamaye kowanne bangare na kasar a dai dai lokacin da ake cika shekaru uku tun bayan da aka sace ‘yan matan na Chibok.
Cikin wani rubutatcen bayani da shugaba Buhari ya yi yace gwamnati na bin sawu da kuma daukar matakan da suka kamata domin samun nasarar cimma alkawuran da aka yi lokacin da gwamnatinsa ta hau karagar mulki.
Da yake karin haske game da bayanin na shugaba Buhari ga ‘yan Najeriya dangane da ‘yan matan Chibok da kuma ayyukan ta’addancin kungiyar Boko Haram a Arewa maso Gabashin kasar, Mallam Garba Shehu, yace shugaban na nuni da cewa an samu ci gaba kan yaki da ta’addanci.
Kasancewar yanzu an kakkabe duk yankunan dake karkashin Boko Haram, abin da ya rage yanzu shine sharar fage inji Mallam Garba Shehu. Baya ga haka kuma akwai kasashe da ke taimakawa wajen samar da tattaunawa tsakanin gwamnati da kuma wadanda ke rike da ‘yan matan Chibok da sauran ‘yan kasar da aka sace.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Umar Faruk Musa.
Your browser doesn’t support HTML5
DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n
Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU