Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan Ya Musunta Zargin Da Aka Yi Masa Na Karbar Rashawa


Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Tsohon shugaban tarayyar Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya musunta zargin da aka yi masa na cewa ya karbi wasu makudan kudade lokacin da suka sayarwa da kamfanin Shell da Eni wata rijiyar Mai a yankin Niger-Delta.

A wata sanarwa mai dauke da saka hannun mai magana da yawun tsohon shugaban kasar Najeriya, Ikechukwu Eze, ta ce wannan zarge-zargen labarin kage ne kawai wadanda aka kirkiro da su domin batawa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan suna a idon duniya.

Sanarwar dai ta bayyana cewa Goodluck Jonathan bai san tsohon ministan Man Fetur din Najeriya ba, Dan Etete, wanda shine ya hada wannan yarjejeniyar mai cike da rudani. Wanda kuma ya karbi makudan kudi daga hannun kamfanonin Mai musamman na Shell, a cinikin rijiyar Man.

Rijiyar Man ta OPL 245 dai anyi imanin itace rijiyar Man da tafi kowacce girma a nahiyar Afirka. An dai yi amfani da wani kamfani mai suna Malabu, wajen karkatar da kudin da aka sayi rijiyar Man dake gabar ruwan Niger-Delta.

Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, ta shigar da kara inda ta ke zargin kamfanin Mai na Shell da wasu kamfanoni da aikata laifin cin hanci da rashawa, sai dai ana sa ran ranar 13 a wannan wata ne kotu zata saurari karar.

Domin karin bayani saurari rahotan Lamido Abubakar Sokoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG