Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Dake Tattare Da Kudaden Da EFCC Ke Kwato wa


EFCC Ta Sake Kama Biliyoyin Naira a Legas
EFCC Ta Sake Kama Biliyoyin Naira a Legas

Cikin kwanaki uku hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa ta kama sama da kudi Naira biliyan 15 a wurare uku a birnin Legas, a ci gaba da ganin nasarar da hukumar ke kara samu kan tsarin nan na ba da tukwici ga wanda ya fallasa wata almundahana.

A sanarwar da hukumar EFCC ta aikawa manema labarai tare da hotuna ta bayyana makudan kudade da suka hada da dalar Amurka da kudin Ingila da Nairori sabbi a nade cikin akwatuna daban-daban da jimillarsu ya kai Naira biliyan 15.

An kama kudaden ne a gida mai lamba 16 dake layin Osborne a unguwar Ikoyi dake cikin Legas.

Ana kirga wasu cikin kudaden da aka kama
Ana kirga wasu cikin kudaden da aka kama

Wani na kusa da hukumar da bai so a ambaci sunansa ba ya ce ana kayautata zaton kudin mallakar wani tsohon jami'in ma'aikatar kamfanin man fetur din kasar ne, wato kamfanin NNPC.

Shi dai jami'in an dade ana bincikensa saboda bacewar wasu kudade.

Binciken da Muryar Amurka ta gudanar ya nuna cewa al’umar Najeriya da dama, na ba da shawarar cewa gwamnatin ta rike wadannan kudade ta gudanar da ayyukan jama’a.

Amma masana tattalin arziki da shari’a na cewa gwamnati ba za ta yi yin gaban kanta ta yi amfani da wadannan kudade kai tsaye ba, kamar yadda masanin tattalin arziki Alhaji Kasimu Kurfi ya fada wa Muryar Amurka.

“Akwai tsari wanda shugaban kasa ya nema wanda ‘yan majalisa ya kamata su amince kan irin wadannan kudade domin a fara amfani da su.” In ji Kurfi.

Kudaden da aka kama
Kudaden da aka kama

​Domin jin karin bayani saurari wannan rahoto daga wakilinmu a Legas Babangida Jibril wanda ya kunshi kalubalen dake tattare da matsalolin dake hana taba irin wadannan kudade kai tsaye da kuma sauran batutuwa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:11 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG