Nan bada dadewa ba ake sa ran gwamnatin shugaba Donald Trump za ta sanarwa da Majalisar Dokoki a hukumance kudurin Amurka na sayarwa Najeriya manyan jiragen yakin nan da ake yayi A29 Super Tucano.
A baya dai Amurka ta yi ta sa tarnaki wajen sayarwa Najeriya makamai bisa zargin dakarun ‘kasar na take hakkin bil Adama, a dai dai lokacin da mayakan kungiyar Boko Haram ke rawar gaban hantsi.
Shi dai wannan sabon jirgin na A29 Super Tucano da ake yayi ya banbanta da wanda yanzu haka dakarun Najeriya ke amfani da shi, kasancewar zai iya hango makiya daga nesa ya kuma kai musu hari ko dare ko rana, haka kuma manyan bindigogin nan na kakkabo jiragen sama basa iya tasiri a kansa.
Wannan mataki dai na gwamnatin Donald Trump ya zo da mamaki ga mafi yawan ‘yan Najeriya, sai dai gogaggen jami’in diplomasiya Ambasada Sulaiman Dahiru, yace bai yi mamaki ba kasancewar ‘yan jam’iyyar Democratic Party sun fi bayar da muhimmanci kan wannan batu, amma ‘yan jam’iyyar Republican basu cika damuwa game da irin wadannan abubuwa ba.
Gwamnatin Najeriya dai ba ta nemi wannan bukata daga gwamnatin Amurka ba, tun lokacin shugaba Goodluck Jonathan aka nemi wannan bukata yayin da Amurka ta sa ‘kafa ta shure a wancan lokacin.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
DOMIN KARIN BAYANI
Kalli cikakkun faya-fayen bidiyo na “Boko Haram: Fuskokin Ta’addanci http://bit.ly/2kT7h6n
Boko Haram: Fuskokin Ta'addanci http://bit.ly/2lujeAU
Facebook Forum