Shugaban Asusun tallafawa yara na MDD da ake kira UNICEF Mr. Geoffrey Ijumba, shine ya shaidawa manema labarai lokacin da yake bayani game da cikar shekaru uku da sace ‘yan matan Chibok.
Mr. Ijumba, yace cikin shekarar 2015 kuma ‘kananan yara guda 56 ne aka yi amfani da su wajen kunar bakin waken, yayin da aka yi amfani da wasu guda 30 cikin shekarar 2016. Sannan wasu ‘yan kunar 27 suka kai hare-hare cikin jama’a a farkon wannan shekarar, wanda hare-haren ke nuni da cewa hare-haren sun fi dukkan hare-haren da suka afku a shekarun baya.
Rikicin Boko Haram dai ya raba yara dayawa da iyayensu da kuma tauye musu damar neman ilimi, duk da cewa yanzu haka ana ta kafa makarantu masu zaman kansu a sansanonin ‘yan gudun hijra daban-daban.
A cewar shugaban UNICEF din yanzu haka akwai yara kusan Miliyan uku da basa zuwa makaranta, haka kuma akwai wasu yaran da yanzu haka ke fama da karancin abinci mai gina jiki da akayi kirasin cewa sun kai rabin Miliyan.
Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.
Facebook Forum