Bayanai Na Kara Fitowa Akan Batun Zaben Amurka

Trump da Putin

An sake bayyana rahoton kasancewar karin mutane a taron da aka yi a katafaren ginin nan na Trump Tower, a watan Yunin 2016 tsakanin mambobin kwamitin yakin neman zaben Trump da wata Lauyar Rasha,

Rahotoni na nuni da cewa akwai karin mutane a taron da aka yi da wata Lauyar Rasha, a cigaba da ce ce ku cen da ake yi kan ko shin kwamitin yakin neman zaben Trump ya hada kai da Rashawa don canza alkiblar zaben Shugaban kasar Amurka.

Jiya kafafen yada labarai sun bayyana cewa wasu Amurkawa 'yan asalin kasar Rasha - - Anatoly Samochornov da Rinat Akhmetshin -- sun bi lauyar ta Rasha zuwa wurin taron, wanda da farko babban dan Trump ya ce taro ne kawai kan batun hana Amurkawa rikon yara haihuwar Rasha.

A wannan satin babban dan na Trump ya ce ya halarci taron ne saboda an masa alkawarin cewa za a bashi wani bayani na wata babbar tabargaza game da abokiyar karawar Trump, Hillary Clinton.

Rinat Akmetshin ya tabbatar ma jaridar Washington Post jiya Jumma'a cewa ya halarci taron, bayan da wasu majiyoyi su ka tsegunta hakan. Gidan Talabjin na MSNBC ya ruwaito da daren jiya Jumma'a cewa Samochornov, wanda tafinta ne, shi ma ya kasance a wurin. An yi imanin cewa ya taba yi ma Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka aiki a matsayin manajan shirye-shirye.