Batun 'Yan Matan Cibok Ina Aka Kwana?

Iyayen da ‘yan uwan ‘yan matan da aka sace suna maida jawabi a taron da suka yi da gwamnan jihar Borno, a Chibok, jihar Borno, 22 Afrilu 2014.

An bukaci a kara jami'an tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya domin cimma burin tsaro a wannan yanki.
Dan majalisar wakilai Muhammad Tahir Monguno yayi kira ga gwamnatin taraiya da ta kara yawan jami’an tsaro wanda suka hada da ‘yan sandan cikin gida da kuma kayan aiki a yankin arewa maso gabashin Najeriya, domin samo 'yan matannan su sama da 200 da 'yan bindiga suka sace a lokacin da suke rubuta jarrabawar karshe a makarantarsu ta Sakandare.

Mr. Monguno mai wakiltar mazaban Monguno Martai Nganze ne yayi wannan furucin a hira da yayi da wakiliyar muryar Amurka Medina Dauda, a birnin tarayya Abuja.

Da yake bayani akan ‘yan matan da aka sace, cewa yayi ”yan matan da aka sace a Cibok, jiya-jiyannan na ji labari anyi mani waya daga mazaba ta cewa an gansu a wani gari Suwaram. Daga Cibok zuwa mazaba na akalla ya kai kilomita dari biyu”

Dan majalisa Monguno ya kara da cewa ”to kilomita dari biyu ana tafiya da wadannan mata haka ba’a gansu ba, kin ga akwai babban matsala wajen tsaro a Najeriya.”

Wakili Mungono na fata jami’an tsaro zasu dauki matakan da suka kamata domin cimma buri na ganin cewa an kubuto da ‘yan matan tunda an gansu.

Ya kuma ce shugaban kasa Jonathan na sha'awar sabonta dokar tabaci, amma baya gani cewa zai samu goyon bayan majalisa.

.

Your browser doesn’t support HTML5

Batun 'Yan Matan Chibok Ina Aka Kwana - 9'24"