Batun Cin Hanci a Zaben Gwamnan Jihar Yobe ya Kunno Kai

Gwamna Ibrahim Gaidam

Zarge zargen cin hancin miliyoyin Nairori ne ya mamaye sharia’ar gwamnan jihar Yobe da akeyi a babban birini tarayyar Najeriya, Abuja.

Ita dai jam’iyuyar PDP, a Jihar Yobe, da wanda yayi mata takarar Gwamna a zaben daya gabata Adamu Maina Waziri, ta bakin Lauyan su babban Lauyan najeriya, Abiodun Oreikoko na zargin wani jami’in Gwamnati mai suna Zakari Deba da baiwa shugaban hukumar zaben jihar na goro.

An dai samasa Naira Miliyan takwas a asusun ajiyarsa na kashin kasa dake bakin Diamond, da wasu Karin Naira miliyan bakwai a asusun sa dake bakin Zenith ranar takwas ga watan Afirilun wannan shekara wato kwanaki ukku kennan kafin zabe.

Kotun dake karkashen jagorancin mai sharia Mojisola Dada, ta gyayato bankuna biyu daga Damaturu zuwa Abuja domin bada shaida.

Bankunan sun gabatarwa kotun wasu mahimman takardun bayanai na asusun da ake Magana akai.

Da yake amsa tambayar lauya mai kara Barrister Abiodun Oreikoko, jami’an bankin Diamond reshen Damaturu Babaji Kukawa, yace kafin ranar da aka sanya wadannan kudade Naira 28,143,60, ne kachal a cikin asusun, bayan an sanya kudin ne kuma sai aka cire inda aka maida kudin asusun wani kamfani .

A bangaren sa Lauyan dake kare jam’iyyar APC, da Gwamna Ibrahim Gaidam, babban Lauyan Najeriya, Yusuf Ali, ya tambayi jami’an bankunan biyu cewar shin ko banki na daukar hoton wanda duk yazo zai sanya kudi a wani asusu inda suka amsa da cewa a’a, yace kowa na iya sanya kudi a kowane asusu batare da mai asusun ya sani ba.