Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari da Tsarin Tattalin Arziki Irin na Gurguzu Inji PDP


Jam’iyyar PDP, mai adawa a Najeriya, ta suke tsarin babban bankin Najeriya, na hana mutane iya shigar da kudi ma’ajiyar kudaden su ta ketare a bankuna. da hakan tace ya kawo tarnaki ga harkar kasuwanci.

Kakakin PDP, Oliseh Metuh, ya zargi Gwamnatin Buhari da cewa tana kokarin kawo tsarin tattalin arziki irin na gurguzu ta hanyar takaita hanyoyin shige da fice kudade ta hannun ‘yan kasuwa.

Duk wannan ma inji PDP, ya samo asalin ne ga rashin samun kwamitin tattalin arziki a wata na ukku tun bayan amsan mulkin da APC, tayi a karshen watan Mayu.

Metuh, yace da ganga shugaba Buhari yaki sanya ‘yan kKasuwa a tawagar sa a lokacin da yakai ziyara Amurka, da haka a ra’ayin PDP, ya sanyaya gwiwar masu son zuba hanayen jari anan Najeriya.

Wannan takaita zuba Dala, ko ma’amala da ita a bankunan Najeriya, yasa dala ta fado da kusa fiye da Naira talatin.

‘Yan rajin kare APC, irin su Aminu Madaucin Bakori, na ganin PDP, na fargaban gyare gyare ne da shugaba Buhari, keyi.

Yanzu dai kusan kullum PDP, kan fida wani martini na kalubalantar Gwamnatin Buhari, idan ka dabe kan lammuran tsaro da PDP, ke cewa bazata sanya ra’ayin siyasa a yaki da ta’addanci ba.

XS
SM
MD
LG