Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Fasa Kwauri Sun yi Hasarar Fiye da Miliyan 250


Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar
Shugaban Hukumar Kwastam ta Najeriya, Abdullahi Dikko Inde, tare da wasu manyan jami'an hukumar

Duk da hana shigowa da naman kaji dana Talo Talo da Gwamnatin Najeriya, tayi masamman ma dan lafiyar alumanta wasu masu fasa kwauri sun shigo dasu.

An kiyasta kudaden kayayyakin da aka kama daka hannun masu wannan ta’annati na fasa kwauri, wanda ya kasance hasara garesu fiye da miliyan dari biyu da hamsin{250}.

Amma hukumar kwastam dake kula da jihohin Oyo da Oshun ta kama manyan motoci shake da Shinkafa Magunguna Tayoyi da naman Kaji da kuma na Talo Talo na miliyoyin Nairori, Muhammad Sulaiman Bawa, mai kula da hukumar ta Kwastam shiyar kudu maso yammacin Najeriya, yace kayayyakin da aka kama an shigo dasu ne batare da bin ka’ida ba wasu ma an hana shigowa dasu.

Ya kara da cewa muddin mutane basu daina shigowa da wadannan abubuwa ba to tabbaci hakikia ba za’a fasa kama su ba inji jami’in na Kwastam.

XS
SM
MD
LG