Majalisar Dattawan Najeriya, ta tabbatar da nadi jami’an tsaron Najeriya, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya nada a watan jiya bayan da ya sauke wadanda ya gada .
Koda yake ‘yan majalisar sai da suka kwashe awowi biyar suna tantance jami’an tsaron, Sanata Kabiru Gaya daga jihar Kano, ya bayana dalilan da yasa aka dauki tsawon lokaci wajen tantance jami’an.
Yace” ba dan komai ba saboda munga irin wahalar da muka shiga a baya dangane ‘yan ta’adda wannan yasa dole ne mu bincike su muyi masu tabbayoyi masu yawa har sai mun gamsu kuma Alhamdulillahi mun gamsu da irin bayanan su kuma muna fatan shawarar da muma muka basu za suyi aiki dasu."
Idan za’a iya tunawa a watan da ya gabata ne shugaba Muhammadu Buhari, ya nada sabin hafsoshin Soja Najeriya bayan sauke wadanda ya gada.