Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayaba da Akuyoyi Zasu Maidaini Likita a Rayuwa


matashi mai tallar ayaba
matashi mai tallar ayaba

Abun bansha’awa da kowane yaro, shine yazama yana da tunanin ko burin mai zai zama a rayuwasa. Domin tahaka ne kawai yaro zai kokarta wajen ganin ya cimma burinsa. Isma’il Muhammad, wani matashi ne mai burin yazama Alkali ko likita, idan Allah yasa ya girma, amma baban abun sha’awa dashi a nan shine, baya makarantar boko a yanzu, amma yana da tunanin idan Allah yasa ansashi to zai kokarta wajen ganin ya maida hankali don cimman burinsa a rayuwa.

Wanda ta haka ne zaka ga cewar duk wani yaro da ya fito daga irin wanna gidan, da yazamana yana da burin yin wani abu, to zai zamo wani abu da kowa zai yi koyi dashi.

A yanzu dai Isma’il yana tallan ayaba ne wanda iyayenshi ke daura mishi, a cikin wanna talla da yake yi, har yasamu ya iya siyama kanshi Akuya wanda ta haifi ‘yaya biyu, wanna yasa yana da tunanin ya sake siyan wasu don ya samu garge maiyawa. Kana ya kuma yi kokarin zuwa makaranta. Abun la’akari dashi a nan shine duk wanda ke da irin wanna tunanin, to za’agacewar zai bada kaimi wajen inganta sana’arshi don yana da wani abu da yake burin samu a rayuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG