Wani bincike ya nuna cewa ana iya amfani da batirin wayar hannu dana karamar komfuta wato laptop domin satar bayanan masu amfani dasu.
Manhajar API da ake amfani da ita cikin na’urorin biyu domin gano yanayin batiri, missali ganin idan yana da caji ko bashi da isashashshan caji, to yanzu haka ana iya amfani da manhajar wajen bibiyar duk abubuwan da mutane keyi akan wayoyin su ko komfutar su ta tafi da gidan ka.
Kasancewar an kirkiri batirin ne da wani fasali da zai ke aika ire-iren wadannan bayanai, hakan ne ya baiwa masu kutse damar tattara bayanai daga mutane, kai harma ganin duk abin da mutane keyi cikin na’urorin su.
Lukasz Olejinik da Gunes Acar, sun fito ne daga kasar Faransa da Belgium wanda sune suka gundanar da wannan binciken. Sun bayyana cewa yana da wahala mutane su kaucewa ire-iren wadannan kutse da ake na satar bayanan su, inda dai har suna amfani da baturan, sun kuma nuna cewa mutane nan dake amfanin da tsofaffin batura sunfi shiga cikin hatsarin kutse.
Sun kuma bayar da shawarar ta yadda za’a iya kaucewa shiga wannan hali, inda sukace rage karfin fitar da bayanai na batiri shine hanya mai sauki da zata hana kutse faruwa.