A zahiri, jam’iyyun sun rabe gida biyu, masu mara baya ga PDP mai mulki na cewa a jinkirta, ko a dage zaben, ma’abota jam’iyyar adawa ta APC na cewa a’a, a gudanar da zaben.
Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP Uche Sakondos, yace ba’a yiwa jam’iyyar shi adalci ba idan aka ce sunce a dage zabe, manufarsu shine a duba lamuran tsaro, a jinkirta zaben.
Abubakar Abdullahi Sokoto, shine Sakataren Jam’iyyar UPN ta Najeriya “jam’iyyata ta yarda a zakudar da zaben, sati daya, ko sati biyu. Kar a bada wannan sati shida.
Da Muryar Amurka ya tambayi Abubakar Sokoto ko basu yi la’akari da zargin da za’a yi musu ba, na cewa sun hada kai da jam’iyya mai mulki PDP, shine yace “a’a, kowa yazo ne, kana da jam’iyya, Jega ya baiwa kowa damar fadar ra’ayinsa”.
Dr. Sadiq Abubakar Gombe, shine Sakataren Jam’iyyar SDP dake watsi da dalilan jinkirta zaben.
“Jam’iyyu goma sha biyu daga cikinmu, mun tabbatar da cewa dole a yi zabe. Mun cewa INEC bamu yadda ba, kuma ba hurumin mu bane”, a cewar Dr. Gombe.
Yunusa Tanko dake jagorantar Zauren Bada Shawarwari ga Jam’iyyun Siyasa na nuna shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega shine yake da wuka da nama.
Farfesa Jega dai a halin yanzu ya shiga taro da Kwamishinonin Hukumar domin samar da matsaya. Za’a iya cewa komai na iya faruwa. Idan ba’a manta ba, a zaben shekara ta 2011 hukumar zaben ta taba dage zaben bayan an fara kada kuri’a.
Your browser doesn’t support HTML5