KADUNA, NIGERIA - Babbar kotun jihar Kadunan da ke sauraron karar da al'umomin wasu garuruwa 12 na karamar hukumar Igabi su ka shigar, su na zargin rundunar sojin da ke Jaji da hana su zuwa gonakin su, ta ce ta kara bada umarnin barin manoman yankin su dangana da gonakinsu idan kuma ba haka ba to za su gamu da fushin kotu.
A hirar shi da Muryar Amurka, Barista Ibrahim Haruna Hamisu, daya daga cikin layoyin da ke kare al'umomin da su ka shigar da wannan kara, ya yi bayani kan hukuncin da alkaliyar kotun, Mai-shari'a Hannatu Balogun ta yanke a zaman kotun na jiya Alhamis.
Ya ce, alkaliyar kotun ta yi alkawarin cewa, idan har jami'an sojin da ke Jaji ba su baiwa manoman da su ka shigar da wannan kara damar zuwa gonakin su ba, to za ta bada umarni kamo su.
Sai dai lauyan rundunar sojin dake Jaji, Barista Ali Ibrahim Omachi ya ce bai da masaniyar cewa sojojin Jajin sun hana masu karar zuwa gonakin su.
Ya ce "ban tabbatar da wannan batu daga wadanda na ke karewa ba, amma daga bayanan da na ke samu ,manyan jami'an sojin dake Jaji ba su takura ko hana kowa zuwa gona ba, sai dai ko ma menene zan koma ga rundunar sojin da na ke karewa don nanata masu shawara ta cewa su kiyaye hukuncin kotun ta hanyar barin al'umomin zuwa gonakin su".
Garuruwa 12 ne ke karar rundunar sojin dake Jaji kan toshe musu hanyoyin zuwa gonakin su, shi ya sa suka cika harabar kotun don bayyana halin da su ke ciki.
Yanzu dai babbar kotun dake jihar Kaduna ta dage zaman ta zuwa 10 ga watan gobe, kuma manoman na sa ran ganin sun sami damar zuwa gonakin su kafin zaman kotun na gaba kamar yadda kotun ta bada umarni.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5