Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Daukar Matakan Magance Takaddama Tsakanin Makiyaya Da Manoma


Taron Manoma a Zinder
Taron Manoma a Zinder

Makiyaya da manoma a jihar Jigawa, Najeriya, sun fara tsokaci dangane da yarjejeniyar da hukumomin jihar da na Jihar Zinder a Jamhuriyar Nijar suka sanya wa hannu domin wanzar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyayan da ke zirga-zirga a sassan jihohin biyu da ke makwaftaka da juna.

Bayan wani taro na yini uku a Dutse babban birnin jihar Jigawa wanda masu ruwa da tsaki daga jihar Zinder da Jigawan suka halarta, an tattauna kan matakan magance matsalolin da ke haifar da takaddama tsakanin makiyaya da manoma sakamakon zirga zirgar da makiyayan kan yi da dabbobin su a sassan jihohin biyu.

Alhaji Idris Ya’u Mai Unguwa Jaga, shugaban kungiyar manoman Najeriya reshen jihar Jigawa, wanda ya halarci taron, ya ce akwai bukatar masu ruwa da tsaki su sanya ido sosai domin bibiyar yadda za a rinka aiwatar da kunshin yarjejeniyar domin tabbatar da samun nasara.

Makiyaya
Makiyaya

Su-ma makiyaya wadanda su kayi maraba da kunshin yarjejeniyar sun sha alwashin wayar da kan mambobinsu game da abin da ta kunsa. Alhaji Adamu Idris Babura, shugaban Miyetti Allah a jihar Jigawa, ya ce nan bada jimawa zasu yi gangami daban daban domin fadakar da makiyaya game da alfanun kiyaye ka’idojin yarjejeniyar domin tabbatar da zaman lafiya da manoma.

Mataimakin gwamnan jihar Jigawa Alhaji Aminu Usman ne ya sanya hannu akan yarjejeniyar a madadin gwamnatin jihar Jigawa, yayin da gwamnan Zinder ya rattaba hannu a madadin gwamnatinsa.

Kananan hukumomin Sule-Tankarkar da Maigatari da kuma Birniwa a Jihar Jigawa na kan gaba wajen fuskantar rikicin makiyaya da Manoma a duk shekara kuma sune ke kan iyakar Jigawan da Jihar Zinder dake Jamhuriyar Nijar.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG