Ba'a Zaci Samun Karanci Masu Jefa Kuri'a Ba

Ma'aikacin zabe

Rashin fitowar masu kada kuri'a masu yawan ne yasa hukumar zabe kara lokaci.
Anci gaba da bude rumfunan zabe a yau laraba,domin baiwa al’ummar kasar Misra damarsu ta zaben sabon shugaban kasa.

Laraba ce ranar da aka kara domin karfafa gwiwar masu son zuwa rumfunan zabe a dai-dai lokacin jami’an gwamnati ke karfafa gangamin gwiwar da su fita su jefa kuri’arsu a zaben da ake kyautata cewar tsohon jagoran rundunar sojojin kasar Misra Abdul-Fatah el-Siissi ne zai kai ga samu nasara.

Masu fashin baki sun bayyana cewar ba'a zaci samun karancin masu jefa kuri'a a kwanaki biyun farko da aka kebe domin gudanar da zaben ba, hakan ne yasa hukumar zaben kasar tayi karin rana guda,amma duk da hakan ba'a cincirindon masu son kada kuri'a a layin rumfunan zaben a yau ba.

Rashin fitowar masu kada kuri'a masu yawan ne yasa hukumar zabe kara lokaci domin baiwa kowa isasshen lokacin zuwa yin amfani da damarsa ta zaben wanda yake so.