Shugaban kungiyar mai kaifin kishin Islama, Mohammad Badie, da biyu daga cikin mataimakansa za su fuskanci tuhumce-tuhumcen laifin ingiza mummunan tashin hankali a lokacin jerin zanga-zanga tun kafin soji su hambare Shugaba Muhammad Morsi.
Wasu na wa Badie ganin tushen karfin fadar Shugaba Morsi, wanda sojin Misra su ka hambare ranar 3 ga watan Yuni bayan mutanen Masar sun yi kwana da kwanaki suna manya-manyan zanga-zangar nuna rashin jin dadin shugabancinsa.
A halin da ake ciki kuma a jiya Asabar hukumomin Misra sun sake bode kan iyakar tsakanin Misra da Gaza, bayan rufewa ta kwanaki biyar da ta hana dubban Falasdinawa tafiye-tafiya.
Dubban mutane sun yi ta jiran su sami damar shiga Misra ta maketarar Rafa zuwa makaranta ko kuma asibiti. An kuma bayar da rahoton cewa daruruwan Falasdinawa na jiran samin damar komawa gida Gaza.
Ba a san ko har zuwa wani lokaci ne hukumomin Misra za su bar maketarar a bude ba.