Abokin aiki Bello Galadanchi ya zanta da masanin tarihi kuma mazaunin birin Alkahira. Kamar yadda ya fada al'ummar kasar tana kokarin hambarar da gwamnatin soja ta yin anfani da daukan matakan dabarun gargajiya yadda ba za'a rubar da jini ba kamar yadda shi Janaral Sisi ya ke son cigaba da yi. Ya ce suna da hanyoyinsu na gargajiya da suke anfani dasu wurin hambarar da duk wadanda suka yi masu milkin mallaka shekaru dubbai da suka gabata.
Wadannan tsare-tsaren na gargajiya sun hada da hadin kai, su ki bude kantuna kuma masu arziki su janye kudadensu daga bankuna domin su hana gwamnati anfani da arzikinsu. Su na iya kin zuwa ofisoshi. Suna iya kin bude duk wasu ma'aikatu. Duk wasu ayyukoki da suka shafi cingaban kasa zasu tsayar dasu sai dai abun da ya shafi jinkai kamar asibitoci da magunguna.
Dangane da yadda basu yi anfani da wadannan dabaru ba tun can farko suka bari ana yi masu kisan kiyashi sai ya ce hakan ta faru ne domin Janaral Sisi ya raba kawunansu.
Ga karin bayani.