Zanga-zangar da aka gudanar a ranar ta jiya da aka yi wa lakabi da “Jumma’ar Shahidai,” ita ce irinta ta farko da ‘yan kungiyar su ka gudanar cikin kwanakin da su ka gabata, kuma ba ta yi karfi ta fuskar yawa da kuma kuzari kamar zanga-zangar da su ka gabata ba, wadanda wasunsu ma sun kunshi dubban masu zanga-zanga a baya.
Sojoji, bisa jagorancin Janar Abdul Fatah al-Sisi, sun damke jami’an kungiyar ta Ikhwanul Muslimin da dama cikin satin da ya gabata, ciki har da babban malamin kungiyar Muhammad Badie.
An kashe akalla wani dan zanga-zanga jiya Jumma’a a birnin Tanta da ke kusa da gabar kogin Nilu. Jimlar mutane sama da 1,000 ne aka hallaka a tashin hankalin siyasa tun bayan hambare Mr. Morsi, ciki har da daruruwan fararen hula yayin da jami’an tsaro su ka murkushe wasu manyan zanga-zanga biyu, na magoya bayan Morsi a birnin Alkhahira.
Hukumar soji dai ta zargi kungiyar ta ‘yan brothers da ingiza tashin hankalin da ta ce ya yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da dama.